News
Yan Bindiga Sun Sace Daraktoci 6 Na Ma’aikatar Tsaro Ta Kasa
Fargaba ta mamaye ma’aikatan gwamnatin tarayya bayan da yan bindiga suka sace daraktoci shida na Ma’aikatar Tsaron Ƙasa a kan hanyar Kabba–Lokoja.
Rahotanni sun ce an sace su ne a ranar Litinin, 10 ga Nuwamba, 2025, yayin da manyan jami’an ke tafiya daga Legas zuwa Abuja domin jarabawar karin girma.
Kotu Ta Umarci A Kamo Soja Kan Zargin Kisan Jami’in KAROTA A Kano
Majiyoyi sun shaida wa Jaridar vanguard cewa maharan sun yi kwanton-bauna tare da tare ayarin motocin jami’an, inda suka yi awon gaba da su zuwa wani wuri da har yanzu ba a gano ba.
Kungiyar Association of Senior Civil Servants of Nigeria (ASCSN) a wata sanarwa da shugabanta, Shehu Mohammed, da Sakatare Janar Joshua Apebo suka fitar, ta bayyana sunayen daraktocin da aka sace kamar haka:
Mrs Ngozi Ibeziakor
Mrs C.A. Emeribe
Mrs C. Helen Ezeakor
Mrs C.A. Ladoye
Mrs J.A. Onwuzurike
Mrs Catherine O. Essien
Sanarwar ta kara da cewa, dukkansu ma’aikatan Command Day Secondary School (CDSS) Ojo, Lagos ne, kuma mambobin kungiyar kwadago.
Harin ya sake nuna karuwar matsalar garkuwa da mutane a kan manyan titunan Najeriya, lamarin da ke ci gaba da zama barazana ga jami’an gwamnati da sauran matafiya.
-
News5 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
-
News4 days ago
ICPC Ta Wanke Femi Gbajabiamila Daga Zargin Badakalar Hukumar Bogi
-
News5 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Dakile Yunkurin Sace Jariri Da Wasu Ma’aikatan Asibiti A Jigawa
