News
An Kubutar Da Mata Da Kananan Yara 46 Da ’Yan Bindiga Suka Sace A Katsina
An kubutar da mutane 46 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Bakori ta Jihar Katsina, bayan tattaunawar zaman lafiya da aka yi ƙarƙashin shirin Operation Safe Corridor.
Bayanan da Zagazola Makama ya tattara sun ce waɗanda aka sako sun haɗa da mata da kananan yara da aka yi garkuwa da su daga kauyukan Guga, da Doguwar Dorawa Fulani settlement, da kuma Gidan Danmayaki.
Majalisar Dattawa Ta Bukaci Daukar Karin Sojoji 100,000 Domin Dakile Matsalar Tsaro
A cewar rahoton, an sako dukkanin waɗannan mutanen ne da misalin ƙarfe 2 na rana, ta hannun wani wanda ake ganin shugaban tawagar ’yan bindiga ne mai suna Isiya Kwashen Garwa, wanda ya shiga tattaunawar sulhu da jami’an tsaro.
Da zarar an sako su, an karɓe su ne daga hannun jami’an tsaro zuwa wajen ɗan majalisar da ke wakiltar ƙaramar hukumar Bakori a majalisar dokokin Jihar Katsina, wanda ya tura su zuwa Cibiyar Kiwon Lafiya ta Bakori domin duba lafiyarsu bayan tsawon lokaci a hannun masu garkuwa da mutane.
Mahukunta sun tabbatar da cewa dukkan waɗanda aka sako sun haɗu da iyalansu kuma an fara kula da lafiyarsu.
Jami’an tsaro da shugabannin al’umma kuma na ci gaba da sa ido domin tabbatar da zaman lafiya da kuma hana sake faruwar makamancin hakan a yankin.
