Connect with us

News

Fiye Da Mutane Miliyan 45 A Nijeriya Har Yanzu Suna Yin Bahaya A Waje — Gwamnatin Tarraya 

Published

on

ce55e3a52e3b0bcf43505b8bbc6e97152a58e04095e0ce71a349d76013d52a3b

Gwamnatin Tarayya ta ce matsalar rashin bandaki a Najeriya na kara ta’azzara, inda sama da miliyan 45 na ’yan kasa ke ci gaba da yin bahaya a waje.

Ministan Muhalli, Balarabe Lawal, ya bayyana hakan a Abuja yayin taron manema labarai na bikin Ranar Bandaki ta Duniya ta 2025, wanda aka yi da taken “Tsabtace Muhalli a Duniyar da ke Canzawa”.

Advertisement

Gwamnatin Kwara Ta Rufe Makarantu A Kananan Hukumomi 4

‎Ministan — wanda Sakataren Dindindin, Mahmud Kambari, ya wakilta — ya ce matsalar ta zama barazana ga lafiyar jama’a da muhalli, inda ya bayyana cewa kashi 25 cikin 100 na ’yan Nijeriya kawai ke da damar yin bahaya a wurare masu tsafta.

‎“A duniya akwai biliyan 4.2 da ba su da bandaki mai aminci. A Najeriya kuma sama da miliyan 45 har yanzu na fitar da bahaya a fili,” in ji shi.

Advertisement

‎Ministan ya nuna damuwarsa kan yadda makarantu, asibitoci da hukumomin gwamnati da dama ko dai basu da bandaki kwata-kwata ko kuma suna amfani da wadanda ba a kula da su.

‎Ya ce har yanzu wasu manyan birane na dogaro da tsofaffin magudanar sharar da ke gaza aiki, abin da ke janyo zubar ruwan datti zuwa koguna da rafuka — lamarin da ke iya janyo cututtuka.

Advertisement

‎Ya kara da cewa rashin tsafta na taimakawa yaduwar cututtuka kamar kwalara, gudawa, typhoid da kuma cututtukan tsutsotsi, wadanda ke kashe dubban mutane a duk shekara, musamman yara ƙasa da shekara biyar.

‎Ya ce wannan matsala na iya jinkirta kokarin Najeriya na cimma manufar SDG 6.2, wadda ta shafi tsaftar muhalli da ingantaccen bandaki ga kowa.

Advertisement

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending