Connect with us

News

Dalilan Da Suke Kawo Sake Ƙaruwar Hare-Hare Kan Makarantu A Arewacin Najeriya ‎

Published

on

f65010f0 c70d 11f0 bf54 19350076d666.jpg

A yayin da ake ci gaba da jimamin sace dalibai mata 25 a Jihar Kebbi a makon da ya gabata, an sake samun wani hari a Jihar Neja, inda ’yan bindiga suka afka wata makarantar kwana suka sace ɗalibai, lamarin da har yanzu ba a tantance adadinsu ba.

‎Wannan sabon lamari na zuwa ne duk da tabbatarwar gwamnatin tarayya cewa tana daukar matakan da suka dace don hana hare-hare a kan makarantu, musamman a yankunan Arewa da suka daɗe suna fama da matsalar tsaro.

Advertisement

Jami’an NDLEA Sun Kama Mutum 230 Da Zargin Ta’ammali Da Miyagun Kwayoyi A Kano

‎A ’yan makonnin da suka gabata, sake bullar hare-haren ya tayar da hankalin jama’a, ganin cewa tsawon lokaci ba a fuskanci manyan hare-hare kan makarantu ba. A karo na baya an yi gagarumin sace ɗalibai ne a ranar 9 ga Maris 2024, lokacin da aka tafi da dalibai 286 daga wani makarantar tsangaya a jihar Sokoto.

‎Me Ya Sa Hare-Haren Suka Sake Komawa?

Advertisement

‎Masanin tsaro, Malam Kabiru Adamu, ya bayyana cewa babbar matsalar ita ce yadda ’yan bindiga suka fahimci cewa an rage wa makarantu kulawar tsaro. Ya ce wannan ya sa makarantun suka sake zama wuraren da ba su da kariya sosai.

‎“Akwai raguwar kulawa daga jami’an tsaro. Hakan ya sa maharan ke ganin makarantu a matsayin wuraren da ba a tsare su sosai,” in ji shi.

Advertisement

‎Kudin Fansa na Karfafa Maharba

‎Ya kara da cewa yawan kudin fansar da ake biya idan aka sace ɗalibai na daga cikin abubuwan da ke kara tayar da hankalin maharan.

Advertisement

‎A cewarsa, sace dalibai kan jawo hankalin duniya kuma ya haifar da matsin lamba da kan sa gwamnati ko iyaye su amince da biyan makudan kudaden fansa, lamarin da ke ci gaba da ƙarfafa miyagun kungiyoyi.

 

Advertisement

‎‘Matakan Gwamnati Na Wucin-Gadi Ne’

‎Malam Kabiru ya yi nuni da cewa duk wani mataki da za a ɗauka wajen kare makarantu ba zai yi tasiri sosai ba muddin ba a magance matsalar gungun ’yan bindiga baki ɗaya.

Advertisement

‎“Sai an kawar da maharan gaba ɗaya. In ba haka ba, duk wani tsari na wucin-gadi ne,” in ji shi.

Advertisement

‎Shirin Kare Makarantu Bai Samu Cikakken Aiwtarwa Ba

‎Masanin ya ce akwai bukatar gwamnati ta tashi tsaye wajen aiwatar da tsare-tsaren kare makarantu. Akwai shirin duniya na “Safe School Initiative” wanda aka kaddamar a 2014, bayan sace ’yan matan Chibok.

Advertisement

‎A 2024, gwamnatin Najeriya ta sanar da ware Naira biliyan 112 domin inganta tsaron makarantu, da nufin kare sama da rabin makarantun da ke cikin barazana daga shekarar 2023 zuwa 2026.

‎Sai dai, a cewar Malam Kabiru, shirin bai samu cikakken aiwatarwa ba har zuwa yanzu, haka ma tsarin cikin gida da Najeriya ta kirkiro a 2021 domin tallafawa matakan kariya.

Advertisement

‎BBC HAUSA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending