News
Gobara Ta Lalata Sansanin ’Yan Gudun A Borno
Wata gobara ta tashi a sansanin ’yan gudun hijira na Mafa da ke Jihar Borno, inda ta lalata matsugunan wucin gadi guda 40 tare da kayan abinci da sauran kayan gida.
Kamar yadda rahoton ke nunawa cewar, lamarin ya faru ne da misalin karfe 11:20 na safiyar Laraba.
Dalilan Da Suke Kawo Sake Ƙaruwar Hare-Hare Kan Makarantu A Arewacin Najeriya
An tuntuɓi hukumar kashe gobara ta tarayya da ta Jiha nan take, yayin da ƙungiyoyin sintiri ƙarƙashin jagorancin DPO na Mafa suka taimaka wajen daƙile cunkoson jama’a da kuma hana satar kayayyaki.
Daga ƙarshe rahoton da ke garin na nuna cewar an kashe gobarar ba tare da an samu rahoton raunuka ko asarar rayuka ba.
Har yanzu ba a tantance adadin kadarorin da suka lalace ba, kuma ana ci gaba da bincike kan musabbabin gobarar.
-
News5 days ago
Dakarun Soji Cafke Wani Shugaban ’Yan Ta’adda a Kaduna, Sun Kwato Harsasai 300
-
News6 days ago
Dan Takarar Gwamnan Kano a Jam’iyyar AP Ya Yi Allah-Wadai Da Kisan Gillar Da Aka Yi Wa Dan-Shagamu
-
News17 hours ago
Rundunar ‘Yansanda Ta Yi Gargaɗi Gam Da Yiwuwar Kai Hare-hare Makarantu Da Wuraren Ibada
