Connect with us

News

Yau Shekara 11 Da Tashin Bam A Babban Masallacin Juma’a Na Kano Ana Tsaka Da Sallah  

Published

on

Africa Kano Bombing

Yau Shekara 11 Da Tashin Bam A Babban Masallacin Juma’a Na Kano Ana Tsaka Da Sallah

Ɗaya daga cikin hare-haren tashin hankali da jihar Kano ta taɓa gani a tarihi, shi ne lokacin da ƴan Boko Haram suka tayar da bama-bamai da harbin mai uwa da wabi a Babban Masallacin Juma’a na Birni.

Advertisement

Hon. Da’u Aliyu Abubakar Ya Zama Jakadan Hukumar Kashe Gobara A Kano

Farmakin na ranar 28 ga watan Nuwamban 2014 na cikin miyagun hare-haren ta’addanci da aka gani a tsawon shekarun da Boko Haram ta yi harkokinta ta gama a babban birnin kasuwancin na arewacin Najeriya.

Hukumomi a lokacin sun ce mutane sama da 100 aka kashe a tsararren harin rashin imani da aka kai ana tsaka da taron sallar Juma’a.

Advertisement

Kodayake akwai yiwuwar adadin mutanen da aka kashe a harin ya fi haka.

Rayuwar mutane da yawa ta canza sanadin hare-haren da Boko Haram riƙa kai wa kan jami’an tsaro da fararen hula, talakawa da sarakuna, Musulmai da Kiristoci a faɗin Kano.

Advertisement

 

Hukumomi a lokacin sun ɓullo da matakai iri daban-daban don katse hanzarin mahara kamar taƙaita zirga-zirga da hana fitar dare a wasu lokuta da datse hanyoyi da kafa shingayen bincike da caje masu shiga wuraren ibada da sauransu.

Advertisement

Sai dai bayan waɗancan miyagun al’amura da Kano ta gani a baya, mutane yanzu sun fuskanci gaba, inda sannu a hankali harkoki ke ci gaba da farfaɗowa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending