Connect with us

News

Rashin Tsaro: Najeriya Ta Dakatar Da Ritayar Wasu Manyan Hafsoshin Soji

Published

on

Army Signage 2

Rundunar Sojin Najeriya ta sanar da dakatar da ritayar wasu manyan hafsoshinta, bayan matakin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dauka na ayyana dokar ta-baci kan tsaro a fadin kasar.

A wata sanarwa da rundunar ta fitar, an ce an dauki matakin ne domin ci gaba da amfani da ƙwararrun hafsoshi a wannan lokaci da ake ƙara yawan jami’an , sakamakon yadda matsalolin tsaro suka tsananta a yankuna da dama.

Advertisement

Sojoji Sun Yi Juyin Mulki A Jamhuriyar Benin

Sanarwar ta ce dakatarwar ta shafi hafsoshin da suka kai ƙarshen shekarun aikin su, wadanda a tsarin da aka saba sukan yi ritaya.

Sai dai rundunar ta bayyana cewa duk wanda bai son ci gaba da wa’adi zai iya yin ritaya kamar yadda doka ta tanada. Amma wadanda suka zabi ci gaba da aiki ba za su sami karin girma ko wasu damar ci gaban aiki ba.

Advertisement

Rundunar Sojin ta ce dakatarwar ta na ɗan lokaci ne, kuma za a sake duba ta idan akwai sauyi mai ma’ana a bangaren tsaro.

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Channels TV

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending