Connect with us

News

Kungiyar In’Gausa Ta Jaddada Muhimmancin Kula Da Rayuwar Yara Masu Buƙata ta Musamman

Published

on

maus bukata ta musammam

A ci gaba da bikin ranar masu bukata ta musamman ta duniya, kungiyar In’Gausa, wacce ke kula da masu bukata ta musamman tare da koya musu dabarun dogaro da kai, ta shirya taro domin wayar da kan iyaye kan yadda za su kula da rayuwar yaran da ke da nakasa ko wasu rauni na musamman.

Jaridar Inda Ranka ta ruwaito cewa taron ya  mayar da hankali ne kan muhimmancin bayar da kulawa da dama ga masu bukata ta musamman a cikin al’umma.

Advertisement

Rashin Tsaro: Najeriya Ta Dakatar Da Ritayar Wasu Manyan Hafsoshin Soji

Shugaban kungiyar, Engr. Mustapha Habu Ringim, ya bayyana cewa babban dalilin taron shi ne inganta fahimta tsakanin iyaye da al’umma kan hakkin da ke wuyansu wajen tallafawa yara masu bukata ta musamman.

“Muna son iyaye su fahimci yadda zasu kula da yaran su, su ba su damar shiga harkokin rayuwa yadda ya kamata,” in ji Engr. Ringim.

Advertisement

A nasa jawabi, Prof. Rufa’i Ahmad, ya bukaci gwamnati da ta kara shiga harkokin masu bukata ta musamman, ta tabbatar da dokoki da tsare-tsaren da ke kare su, tare da samar da kayan aiki da horar da ma’aikata a kananan asibitoci.

“Yakamata gwamnati ta sanya ido sosai domin a samu daidaito a kula da su a duk matakai,” in ji Prof. Rufa’i.

Advertisement

Haka kuma, Aisha Ibarahim Ahmad, daga cikin jagororin kungiyar, ta bayyana yadda suke fara kula da yara masu bukata ta musamman tun suna ƙanana, domin tabbatar da ingantacciyar tarbiyya da rayuwa.

“Muna koya musu dabarun dogaro da kai tun suna yara domin su zama masu zaman kansu,” in ji ta.

Advertisement

Uwa ga ɗa mai fama da nakasa, Hajiya Binta, ta ce duk da ƙalubalen da take fuskanta, ba ta gajiya wajen kula da ɗanta, domin tabbatar da cewa yana samun rayuwa mai inganci.

Manufar ware wannan rana, kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana, ita ce kawar da wariya da ba da damar shiga al’umma ga masu bukata ta musamman. Taken bikin bana shi ne: “Ba da Dama da Jagoranci ga Masu Bukata ta Musamman”, wanda ya zama muhimmin bangare na muradun ci gaba mai dorewa da ake fatan cimmawa nan da shekarar 2030.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending