News
Jami’an KAROTA Sun Mika Giya da Su Kama Mai Darajar Miliyoyin Naira Ga Hukumar Hisbah Domin Lalatawa
Hukumar Kula da Hanyoyi ta Jihar Kano (KAROTA) ta mika manyan motoci guda uku dauke da giya mai darajar miliyoyin naira ga Hukumar Hisbah ta Jihar Kano domin rushewa kamar yadda doka ta tanada.
An kama giyar ne yayin sintirin dare na ma’aikatan KAROTA a manyan titunan birnin Kano. Jimillar kwalaben giya 4,920 ne aka samu cikin katuna fiye da 410 da ke cikin motocin, wanda aka shirya rarrabawa a sassa daban-daban na garin.
An Gurfanar Da Tsohuwar Ministar Sufurin Jiragen Sama Kan Zargin Almundahanar Naira Biliyan 5
Da yake jawabi yayin mika kayan, Daraktan KAROTA, Faisal Mahmud Kabir, wanda Alhaji Mahmud Haido, Daraktan Gudanarwa da Sabis na Gabaɗaya ya wakilta, ya ce wannan kamun ya nuna yadda hukumar ke dagewa wajen kare lafiyar jama’a da tsaron gari.
“Daya daga cikin ayyukan KAROTA shi ne sa ido a kan hanyoyi don gano kaya ko abubuwan da ake zargi, da kuma sanar da hukumomin tsaro,” in ji Haido. “Za mu ci gaba da kare jama’a daga abubuwan da ka iya cutar da su.”
Da yake karɓar kayan, Kwamandan Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, wanda Shugaban Sashen Kayayyakin Maye, CSH Sani Nasidi Uba Rimo ya wakilta, ya yabawa ma’aikatan KAROTA bisa kwazo da kwarewa da suka nuna.
Ya tabbatar da cewa za a bi ka’ida kafin lalata kayan, kamar yadda dokokin jihar suka tanada.
Sheikh Daurawa ya jaddada mahimmancin hadin gwiwa tsakanin Hisbah da KAROTA wajen hana yaduwar kayan haram a fadin birnin Kano. Ya kuma roki Allah Ya saka da alheri ga hukumar KAROTA da ma’aikatanta bisa kokarinsu wajen tabbatar da doka da oda a cikin al’umma.
