News
Yawan Yara Masu Cin Gajiyar Inshorar Lafiya A Jihar Kano Sun Kai Sama Da 124,000 – KSCHMA
Hukumar Kula da Tsarin Inshorar Lafiya ta Jihar Kano (KSCHMA) ta bayyana cewa sama da yara 124,802 ‘yan kasa da shekara biyar sun shiga kuma suna cin gajiyar tsarin inshorar lafiyar jihar, a wani yunkuri na kare lafiyar yara da rage mace-macen kananan yara a Kano.
Shugabar hukumar, Dr. Rahila Aliyu Muktar, ta bayyana hakan ne yayin bikin Ranar Kariya ga Lafiya ga Kowa (Universal Health Coverage Day) ta 2025 da aka gudanar a Kano.
Dakarun Soji Sun Dakile Harin ISWAP Kan Sansanin Soji A Borno, Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama
Dr. Rahila ta ce ci gaban ya yi daidai da ƙudirin gwamnatin Jihar Kano na tabbatar da samun ingantacciyar kulawar lafiya ga kowa da kowa, musamman marasa galihu da masu rauni.
Ta ƙara da cewa, shigar yara cikin tsarin inshorar lafiya ya zama ginshiki a manufofin gwamnatin Kano, inda ya bayyana cewa kare lafiyar yaro na nufin kare makomar al’umma baki ɗaya.
A cewarsa, “Yaro da ya samu kulawar lafiya cikin lokaci ba wai kawai ya tsira daga cuta ba ne, har ma yana samun damar girma cikin koshin lafiya da cikakken ƙarfi.”
Tallafin gwamnati da faɗaɗa inshora
Hukumar ta ce yawan masu inshorar lafiya a Kano ya karu zuwa 933,014 daga 497,262 a 2023, wanda ke nuna ƙaruwa da kashi 87.6 cikin 100 a cikin shekaru biyu.
Ta ce wannan ci gaba ya samu ne sakamakon jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, da kulawar Kwamishinan Lafiya, Dr. Abubakar Labaran, tare da tallafin Asusun Kula da Lafiya na Kano (KHETFUND).
Yara da sauran masu rauni
Baya ga yara, shirin inshorar ya rufe:
mata masu juna biyu 145,723,
masu nakasa 46,512,
masu cututtuka masu tsanani 31,003,
masu dauke da HIV 29,473,
da fursunoni 3,609.
Hukumar ta ce wadannan rukuni ne da gwamnati ta ba fifiko domin tabbatar da cewa babu wanda aka bari a baya wajen samun kulawar lafiya.
Shirye-shiryen da ke kare lafiyar yara
KSCHMA ta ce ta aiwatar da tsare-tsare da dama da ke da nasaba kai tsaye da lafiyar yara, ciki har da:
faɗaɗa inshora a cibiyoyin lafiya na matakin farko,
shigar da fasahar zamani domin sa ido kan yadda ake kula da marasa lafiya,
da kuma shirye-shiryen wayar da kai ga iyaye musamman a yankunan karkara.
A ƙarshe, hukumar ta jaddada cewa cimma Kariya ga Lafiya ga Kowa na farawa ne da kare lafiyar yaro, inda ta bukaci iyaye da al’umma su rungumi tsarin inshorar lafiya domin amfanin ‘ya’yansu.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
