Connect with us

News

Jirgin Sama Ya Yi Saukar Gaggawa A Kano

Published

on

Wani jirgin sama mai zaman kansa mallakin kamfanin Flybird ya yi saukar gaggawa a safiyar Lahadi a Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano (MAKIA), bayan tasuwar sa  daga Abuja.

Majiyoyi sun shaida wa Solacebase cewa jirgin, wanda ke ɗauke da mutane 11 ciki har da ma’aikatan jirgi uku, ya gamu da matsala ne yayin sauka da misalin karfe 9:30 na safe, lamarin da ya tilasta yin saukar gaggawa.

Advertisement

Shugaban NUJ Na Ƙasa Ya Jagoranci Buɗe Ofishin Kano Online Media Chapel, Yayi Alƙawarin Inganta Walwalar Ƴan Jarida

Wani shaidar gani-da-ido ya ce an samu nasarar fitar da dukkan fasinjojin lafiya, ba tare da rahoton asarar rai ko munanan raunuka ba.

Lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da nuna damuwa kan batun tsaron zirga-zirgar jiragen sama a Najeriya, biyo bayan wasu makamantan abubuwa da suka faru a baya-bayan nan.

Advertisement

 

— Karin bayani na nan tafe.

Advertisement

 

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending