News
Gwamnatin Kano Ta mika sakon Ta’aziyyar Rasuwar Barrista Maryam Abubakar
Gwamnatin Jihar Kano ta ce ta shiga cikin jimami sakamakon rasuwar Barrista Maryam Abubakar, Daraktar Shirye-shirye a Cibiyar Wayar da Kai kan Adalci da Riƙon Amana (CAJA), wadda rasuwarta ta bar giɓi mai girma a fannin shari’a da ƙungiyoyin farar hula a jihar Kano.
A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya fitar a ranar Litinin, gwamnatin ta bayyana marigayiyar a matsayin lauya mai ƙwarewa wadda ta sadaukar da rayuwarta wajen kare adalci, riƙon amana da haƙƙin mata.
Sanarwar ta ce Barrista Maryam ta taka muhimmiyar rawa wajen inganta bin doka da oda, da kuma yaƙi da rashin adalci a cikin al’umma, musamman ta hanyar ayyukanta a CAJA da sauran ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam.
Gwamnatin jihar, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ta miƙa ta’aziyyarta ga shugabanci da ma’aikatan CAJA, Ƙungiyar Lauyoyin Mata ta Duniya (FIDA), Ƙungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA) reshen Kano da Ungogo, da kuma iyalan marigayiyar.
Sanarwar ta bayyana rasuwar a matsayin babbar asara da za ta yi wahalar cikewa, tare da addu’ar Allah Madaukakin Sarki Ya gafarta mata, Ya sanya ta a Aljannar Firdausi, Ya kuma ba iyalanta da abokan aikinta haƙurin jure wannan rashi.
Sanarwar ta samu sa hannun Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, a ranar 29 ga Disamba, 2025.
