Connect with us

News

Kungiyar Mashawartan Gwamnan Kano Ta Bukaci Yan Siyasa Su Guji Kalaman Da Ka Iya Tayar Da Rikici Ko Haddasa Rarrabuwar Kai A Jihar

Published

on

IMG 20260104 WA0002

Kungiyar Mashawarta na Musamman ga Gwamnan Jihar Kano ta bukaci ‘yan siyasa, masu rike da mukamai da kuma magoya bayan jam’iyyun siyasa da su guji kalamai ko ayyukan da ka iya tayar da rikici ko haddasa rarrabuwar kai a jihar.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren Kungiyar, Dr. Idris Salisu Rogo, ya fitar, inda ya yi tsokaci kan yanayin siyasar Jihar Kano da ke sauyawa a halin yanzu.

Advertisement

‎Kungiyar Likitoci Za Ta Sake Tsunduma Yajin Aiki Daga Ranar 12 Ga Janairu

A cewarsa, siyasa a tsarin dimokuraɗiyya dabi’a ce mai cike da sabani, amma ya kamata a gudanar da ita bisa mutunta juna, ladabi da kishin zaman lafiya domin kare muradun al’umma.

Kungiyar ta bayyana cewa amfani da kalaman hura wuta, cin mutunci, barazana ko tona sirrin tattaunawar kashin kai na iya raunana amincewar jama’a, tare da karkatar da hankali daga manyan al’amuran shugabanci da ci gaban jihar.

Advertisement

Sanarwar ta jaddada cewa Gwamnan Jihar Kano shi ne jagoran gwamnati, kuma shi ke da alhakin yanke muhimman hukunci kan alkiblar siyasar jihar.

Mashawartan sun ce suna goyon bayan duk wani mataki da gwamnan zai dauka domin kare muradin Kano.

Advertisement

Haka kuma, Kungiyar ta tabbatar da goyon bayanta ga manufofin gwamnan da suka shafi inganta shugabanci, bunƙasa ababen more rayuwa, walwalar jama’a da sauye-sauyen da nufin inganta rayuwar mazauna Jihar Kano.

Kungiyar ta yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su fifita zaman lafiya, mutunta juna da muradin Jihar Kano fiye da bukatun siyasa na kashin kai.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending