Connect with us

News

Fadan ’Yan Daba A Kano: Mutum Daya Ya Rasa Rai, ’Yan Sanda Sun Kama Mutum 9

Published

on

FB IMG 1759160530529

Akalla mutum ɗaya ya mutu yayin da ’yan sanda suka kama mutane tara a sakamakon wani rikici mai tsanani tsakanin ƙungiyoyin ’yan daba biyu a wasu unguwannin birnin Kano.

Majiyoyi sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da daren ranar 4 ga Janairu, 2026, a Kawo da Mariri.

Advertisement

Fadan ’Yan Daba A Kano: Mutum Daya Ya Rasa Rai, ’Yan Sanda Sun Kama Mutum 9

Jaridar Daily Post  ta ruwaito cewa  rikicin ya shafi ƙungiyoyi biyu masu gaba da juna, waɗanda Kabalo Snu da Faizu Mohammed, wanda aka fi sani da Chabross, ke jagoranta. An ce rikicin ya samo asali ne daga ramuwar gayya sakamakon wata arangama da ta faru a baya tsakanin waɗannan ƙungiyoyi.

Da misalin ƙarfe 1:40 na rana, Faizu Mohammed ya ji rauni a wani rikici, wanda ya fusata magoya bayan Kabalo, lamarin da ya kai ga harin ramuwar gayya da aka kai da daddare.

Advertisement

A yayin arangamar, an soka wa Faizu Mohammed wani abu mai kaifi a wuya, lamarin da ya janyo mummunan rauni. An garzaya da shi Asibitin Kwararru na Muhammadu Sanusi, inda daga bisani ya rasu yayin da ake yi masa kulawar gaggawa. Bayan mutuwarsa, an mika gawarsa ga iyalansa domin jana’iza, lamarin da ya kawo ɗan kwanciyar hankali a yankunan da abin ya shafa.

Sai dai a safiyar 5 ga Janairu, jami’an tsaro sun sake shiga aiki bayan samun rahotannin taruwar wasu da ake zargin ’yan daba ne a Kawo Quarters, suna shirin kai hari a gidan Kabalo a Jar Kuka, Mariri. ’Yan sanda sun kai dauki cikin gaggawa, inda suka tarar da cewa mutanen sun fasa wani shago mallakin Kabalo.

Advertisement

A sakamakon samamen, an kama mutane tara yayin da wasu suka tsere, sannan an kwato wasu kayayyaki. Jami’an tsaro sun tabbatar da cewa an shawo kan lamarin, kuma harkokin yau da kullum sun koma daidai a yankunan da abin ya shafa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending