Sports
Manchester United vs Liverpool: Za su kece raini a Thailand a Yuli

Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Manchester United za ta fafata da Liverpool a wasan atisayen fuskantar kakar badi da za su kara a Thailand cikin watan Yuli.
Haka kuma kwana bakwai tsakani, United za ta kece raini da Crystal Palace a Australia, idan ta kece raini da kungiyar Anfield.
Kungiyar Old Trafford za ta kara da wadda Jurgen Klopp ke jan ragama a filin wasa na Rajamangala a Bangkok ranar 12 ga watan Yuli.
Daga nan kuma United za ta je Melbourne Victory filin da ke cin ‘yan kallo 100,000 da ake kira Melbourne Cricket Ground ranar 15 ga watan Yuli domin fuskantar Palace ranar 19 ga watan.
Kungiyoyi da dama ba su je wasannin atisayen tunkarar kakar tamaula ba a wasu kasashen a ‘yan shekarun nan, tun bayan bullar cutar korona.
Haka kuma United na fatan nada sabon koci da zai horar da ita a wasannin da za ta buga, idan an karkare kakar bana, bayan da Ralf Rangnick ke aikin rikon kwarya, sakamakon da aka kori Ole Gunnar Solskjaer.
Shugaban Crystal Palace, Steve Parish ya ce ”Muna cike da murna da farinciki da za mu ziyarci Australia a karon farko a tarihin kungiyar.”
-
News6 days ago
Wasu ’Yanbindiga Sun Yi Garkuwa Kimanin Yara 12 A Neja
-
News4 days ago
Majalisar Dattawa Ta Yi Watsi Da Shirin Farfaɗo Da Kamfanin Jirgin Saman Nigeria Air
-
News6 days ago
Jami’an NDLEA Sun Kama ‘Yan Nijeriya Biyu Mazauna Turai Da Suka Haɗiye Ƙunshin Hodar Iblis Guda 200 A Filin Jirgin Abuja
