Connect with us

News

‎Sarkin Jinkan Hausawan Afrika ya yi Allah-wadai da kashe matar aure da ’ya’yanta 6 a Kano ‎

Published

on

IMG 20260119 WA0008

Sarkin Jinkan Hausawan Afrika, Ambasada Ibrahim Ali Ibrahim (Abba Alra-iwas), ya yi Allah-wadai da kisan matar aure da ’ya’yanta shida a Jihar Kano.

‎An kashe Fatima Abubakar mai shekaru 35, tare da ’ya’yanta a gidansu da ke Dorayi Gidan Kwari a ranar Juma’a.

Advertisement

Shugaban Limaman Ilorin Sheikh Muhammad Bashir Saliu Ya Rasu Yana Da Shekaru 75

‎A wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, Ambasada Ibrahim Ali Ibrahim ya bayyana lamarin a matsayin abun tashin hankali, kuma ya ce lamarin ya taɓa zuciyar al’ummar Kano.

‎“Na shiga matuƙar damuwa da girgiza bisa kisan gillar da aka yi wa wata uwa da ’ya’yanta shida a Kano.

Advertisement

‎­“Wannan mugun aiki bai tsaya kan waɗannan mutane ba, ya karya tasirinmu na zaman lafiya da girmama rayuwar ɗan Adam,” in ji shi.

‎Sarkin Jinkan ya kuma miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan marigayiyar da sauran waɗanda lamarin ya shafa, tare da yin addu’a ga mamatan.

Advertisement

‎“Ina miƙa ta’aziyyata ga iyalan mamatan, da al’ummar Dorayi da Chiranchi, da kuma ɗaukacin al’ummar Jihar Kano.

‎“Allah Ya gafarta musu, Ya bai wa iyalansu haƙuri da juriyar jure wannan babban rashi,” in ji shu.

Advertisement

‎Ya kuma yi kira ga gwamnati, hukumomin tsaro, sarakunan gargajiya da shugabanni da su haɗa kai wajen kare rayuka da hana aukuwar irin wannan lamari a nan gaba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending