News
Matsalar Tsaro Da Kuma Lalubo Hanyar Bunkasa Kano Gwamna Abba Kabir Ya Tattauna Da Shugaba Tinubu, Ba Siyasa Ba — Gwamnatin Kano
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gana da Shugaban Ƙasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, a Abuja, inda suka tattauna matsalolin tsaro da kuma kisan wata matar aure da ’ya’yanta shida da ya tayar da hankulan al’umma.
Daraktan yaɗa labaran gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ne ya bayyana hakan, jim kaɗan bayan da aka hango gwamnan yana wata ganawar sirri da Shugaba Tinubu a fadar shugaban ƙasa.
Kotun Tarayya Ta Wanke Mahadi Shehu Daga Dukkan Tuhume-tuhume
A cewar Bature, gwamnan ya yi wa shugaban ƙasar cikakken bayani kan halin da ake ciki na tsaro a Kano, da kuma matakan da gwamnatinsa ke ɗauka domin bai wa jami’an tsaro haɗin kai wajen tabbatar da zaman lafiya.
Ya ce gwamnan ya jaddada aniyarsa ta ci gaba da aiki tare da hukumomin tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Sai dai ganawar ta zo ne a daidai lokacin da ake yaɗa jita-jitar cewa gwamnan Kano na shirin sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC mai mulki, lamarin da ya sa wasu ke zargin cewa batun siyasa ne ke ƙunshe cikin tattaunawar.
Amma fadar gwamnan Kano ta musanta hakan, tana mai cewa babban abin da aka tattauna shi ne batun tsaro da kuma mummunan kisan da ya girgiza al’ummar jihar.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu wata sanarwa daga fadar Shugaban Ƙasa da ke nuna cewa batun sauya sheƙar siyasa na daga cikin ajandar ganawar.
