Connect with us

News

Shugabar AHIP Ta Gargadi Matasa Kan Barin Ƙasa Don Neman Aiki, Ta Buƙaci Su Koya Sana’o’i

Published

on

IMG 20260121 WA0024

Shugabar ƙungiyar African Health Initiative Project (AHIP), Dr. Mairo Bello, ta yi kira ga al’ummar jihar Kano, musamman matasa, da su maida hankali wajen koyon sana’o’i domin dogaro da kansu, maimakon barin ƙasa zuwa ƙasashen waje da sunan neman aiki.

Ta bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da ƙungiyarta ta shirya domin wayar da kan jama’a game da haɗarin da ke tattare da fita ƙasashen waje ba tare da isasshen shiri ko kariya ba.

Advertisement

An Tafi Da Malam Ibrahim Isah Makwarari Gidan Yari Saboda Rashin Cika Sharuɗan Beli

A cewarta, binciken da suka gudanar ya nuna cewa da dama daga cikin matasan da ke barin ƙasa suna fuskantar cin zarafi, muzantawa da wahalhalu a wasu ƙasashe, yayin da wasu ma ke rasa rayukansu sakamakon shiga ayyuka masu haɗari.

“Wasu na fuskantar zalunci da wulakanci, wasu kuma har rayukansu suke rasa saboda irin ayyukan da ake tilasta musu,” in ji Dr. Mairo.

Advertisement

Ta ƙara da cewa ƙungiyar AHIP ta samar da shirye-shirye na koyar da sana’o’in hannu da dabarun dogaro da kai, musamman ga mata, domin su gina rayuwarsu a gida ba tare da buƙatar fita ƙasashen waje ba.

Haka kuma, ta ce za su haɗa matasan da suka ci gajiyar horon da wasu ƙungiyoyi masu zaman kansu da hukumomin gwamnati, domin su samu tallafi da zai taimaka wajen bunƙasa kasuwancinsu.

Advertisement

Wakiliyarmu Safiya Muhammad Usman ta ruwaito cewa taron ya gudana ne da haɗin gwiwar ƙungiyoyi na ƙasa da ƙasa kamar UN Migration, ECOWAS, International Labour Organization (ILO) da kuma Tarayyar Turai (EU).

Taken taron shi ne “Ruth Project”, wanda aka ƙaddamar domin tallafa wa matasa wajen gina makoma mai ɗorewa a cikin ƙasarsu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending