Connect with us

News

Gwannan Abba Kabir Yusuf ya fice daga jam’iyyar NNPP.

Published

on

FB IMG 1769184100322

Gwamnan Jihar Kano Arewa maso Yammacin Najeriya Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar NNPP, yana mai danganta matakin da rikice-rikicen cikin gida da suka dabaibaye jam’iyyar, tare da cewa ya dauki wannan mataki ne domin kare muradun al’ummar jihar Kano.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya rattaba wa hannu kuma aka rabawa manema labarai a wannan ranar Juma’a.

Advertisement

Gwannan Abba Kabir Yusuf ya fice daga jam’iyyar NNPP.

A wata wasika da gwamnan ya aike wa shugaban jam’iyyar NNPP na mazabarsa ta Diso-Chiranchi da ke Karamar Hukumar Gwale, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar tun daga yau Juma’a, 23 ga Janairu, 2026.

Advertisement

A cewar gwamnan, “Na rubuto wannan wasika ne cike da godiya domin sanar da shugabancin jam’iyyar NNPP matsayina na ficewa daga jam’iyyar, wanda zai fara aiki daga ranar Juma’a, 23 ga Janairu, 2026.”

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nuna godiyarsa ga jam’iyyar bisa damar da ta ba shi da kuma goyon bayan da ya samu tun bayan shigarsa jam’iyyar a shekarar 2022.

Advertisement

Gwamnan ya ce jam’iyyar na fama da rikice-rikicen cikin gida, sakamakon sabanin shugabanci da kuma shari’o’i da dama da ke gaban kotuna a sassa daban-daban na kasar nan.

A cewarsa, wadannan rikice-rikice sun haifar da rarrabuwar kai da rashin dunkulewar jam’iyyar a matakin jiha da kasa baki daya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending