News
Kaduna: Dakarun Soji Sun Dakile Harin ‘Yan Bindiga A Maraban Rido
Sojojin Rundunar 1 Division ta Sojojin Nijeriya sun dakile wani hari da ake zargin ‘yan bindiga sun kai a wani yanki na Jihar Kaduna, inda aka hallaka mutum ɗaya daga cikin maharan.
Bayanan da PRNigeria ta fitar sun nuna cewa lamarin ya faru ne a daren 22 ga Janairu, 2026, bayan da jami’an tsaro suka samu rahoton gaggawa kan wasu ‘yan bindiga da suka shiga ƙauyen Anguwan Fulan, a yankin Maraban Rido, inda suka kwashi dabbobin mazauna garin.
Tsohon Ɗan Majalisar Jihar Kano, Zubairu Madobi, Ya Fice Daga Jam’iyyar NNPP
Da samun bayanan sirri, sojoji suka tura dakaru zuwa yankin, inda suka yi masu kwanton ɓauna a hanyoyin da ake zargin maharan za su bi wajen tserewa.
A lokacin da aka yi arangama da su, sojojin sun buɗe wuta, lamarin da ya sa ‘yan bindigar suka watse. Daya daga cikinsu ya rasa ransa yayin musayar wutar.
Majiyoyin soji sun ce bayan arangamar ta farko, dakarun sun ci gaba da bincike a dazuzzukan yankin, ciki har da Dajin Kankomi, domin hana ‘yan bindigar sake haɗuwa ko kai wani sabon hari.
Rahotanni sun ce an sake samun wata arangama a kusa da Anguwan Sarki, inda hakan ya ƙara tarwatsa yunkurin tserewar maharan.
-
News2 days ago
Wasu ’Yanbindiga Sun Yi Garkuwa Kimanin Yara 12 A Neja
-
News2 days ago
Jami’an NDLEA Sun Kama ‘Yan Nijeriya Biyu Mazauna Turai Da Suka Haɗiye Ƙunshin Hodar Iblis Guda 200 A Filin Jirgin Abuja
-
News19 hours ago
Majalisar Dokokin Kano Ta Tsawaita Dakatarwar Da Ta Yi Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomin Rogo, Bagwai Da Bebeji

