Connect with us

News

Gwamnatin Kano ta buɗe sabon aikin magudanar ruwa a Unguwar Badawa

Published

on

IMG 20260125 WA0001

Ma’aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi ta Jihar Kano ta buɗe sabon aikin magudanar ruwa da aka kammala a Unguwar Badawa, da ke mazabar Giginyu a Karamar Hukumar Nasarawa, a wani yunkuri na rage ambaliya da matsalolin muhalli da ke addabar yankin a lokacin damuna.

An buɗe aikin ne a madadin Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi, Dr. Dahiru Muhammad Hashim, wanda Daraktan Tsare-tsare da Kididdiga na Ma’aikatar, QS Shazali Garba Fagge, ya wakilta.

Advertisement

SERAP Ta Maka Ministan Wutar Lantarki Da NBET Kotu Kan Zargin Badakalar N128bn 

QS Shazali Garba Fagge ya ce an aiwatar da aikin ne bisa ƙa’idojin injiniya da tsare-tsaren muhalli, domin sauƙaƙa kwararar ruwa da rage illar ambaliya ga mazauna Unguwar Badawa da kewaye.

Advertisement

“Manufar aikin ita ce tabbatar da ingantacciyar hanyar kwararar ruwa, musamman a lokacin damuna, domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma,” in ji shi.

A nasa bangaren, Injiniya Ibrahim Rufa’i, wanda ya aiwatar da aikin, ya bayyana cewa an kammala aikin cikin nasara ba tare da fuskantar manyan ƙalubale ba, yana mai alaƙanta hakan da haɗin kai da suka samu daga mazauna yankin.

Advertisement

Ya kuma yi kira ga jama’a da su guji zubar da shara a magudanan ruwa, yana mai gargadin cewa toshewar hanyoyin ruwa na iya rage amfanin aikin.

Wakiliyarmu ta ruwaito cewa Mai Unguwar Badawa, Aliyu Isa Barde, ya yaba da aikin, yana mai cewa zai taimaka wajen rage matsalolin da al’ummar yankin ke fuskanta a duk lokacin damuna.

Advertisement

Mai unguwar ya kuma yi kira ga mazauna Unguwar Badawa da su kula da tsaftar muhalli, domin tabbatar da dorewar amfanin aikin magudanar ruwan.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending