News
Ana Zargin Jami’an Ƴansanda Sun Buɗe Wuta A Kan Masu Zanga Zangar Lumana A Lagos
Jami’an Ƴansanda a birnin Lagos dake Najeriya sun yi amfani da hayaƙi mai sa hawaye da kuma harsasai wajen tarwatsa masu zanga zangar lumana da suka je majalisar dokokin jihar domin bayyana ƙorafin su a kan rusa musu gidaje da gwamnatin jihar ta yi.
Rahotanni sun ce mutane da dama sun samu harbin bindiga, inda aka ga jini na zuba a jikin su, kamar yadda Jaridar Premium Times da ake wallafawa a jihar ta ruwaito.
Jihar Kwara Ta Sa Dokar Hana Fita Saboda Matsalar Tsaro
Su dai masu zanga zangar da suka fito daga unguwanni da dama cikin su harda Makoko, inda aka rusawa gidaje, sun je majalisar ne domin sake gabatar da kukan su a kan matakin da aka ɗauka na rutsa matsugunan su da makarantu da kuma kasuwanni, inda suka samu rakiyar ƴanjaridu da ƙungiyoyin fararen hula.
Wani shaidar gani da ido ya ce wasu ƴan majalisu ne suka buƙaci kwamishinan ƴansanda Jimoh Moshood da ya tarwatsa masu zanga zangar tare da ƴan jaridun da suka je majalisar domin ganin yadda za ta kaya.
Ƙungiyar mutanen da aka rusawa gidaje da kuma ƙwacewa filaye a Lagos ta shirya zanga zangar wadda ta fara daga unguwar Ikeja zuwa Majalisar dokokin ɗauke da alluna dake da rubuce rubuce daban daban, ciki harda ‘A kare rayukan mu’, da ‘ A dakatar da kisan da kuma rusa mana gidaje’.
Shugaban masu zanga zangar Hassan Soweto ya ce basa adawa da rusa gidajen, amma suna bukatar a bi ka’ida da kuma kare hakkokin su.
Daya daga cikin fitattun lauyoyin Najeriya Femi Falana ya bayyana damuwarsa a kan yadda gwamnatin Lagos ke ƙin mutunta umarnin kotu dangane da lamarin, la’akari da cewa a watan Agustan bara kotu ta haramta aikin rusa gidajen a Makoko da Oko-Agbon da Sogunro da kuma Iwaya.
Ita dai gwamnatin Lagos ta kare matakin da ta ɗauka na rusa gidajen, inda ta ce dokokin ƙasa sun haramta gida gidaje a hanyoyin ruwa da kuma ƙarƙashin manyan layukan wutar lantarki saboda haɗarin dake tattare da matakin.
Kwamishinan yaɗa labarai Gbenga Omotosho ya ce matakan da suka ɗauka ba su saɓa ƙa’ida ba.
Shi kuwa mai bai wa gwamna shawara a kan raya birane, Olajide Babatunde cewa ya yi rusa gidajen na daga cikin shirye shiryen tabbatar da ƙa’idodin gine gine da kuma kare martabar birnin Lagos.
