Connect with us

News

Tayar Jirgin British Airways Ta Ɓalle Jim Kaɗan Bayan Tashi Daga Las Vegas

Published

on

FB IMG 1769622313244

Wata taya ta bayan jirgin British Airways ta ɓalle jim kaɗan bayan jirgin ya tashi daga birnin Las Vegas na Amurka zuwa Landan, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta bayan bayyana bidiyon da ke nuna faruwar abin.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a daren ranar Litinin, misalin ƙarfe 9:10 na dare agogon yankin, yayin da jirgin, wanda ake zargin Airbus A350-1000 ne, ya tashi daga Filin Jirgin Sama na Harry Reid International Airport da ke jihar Nevada.

Advertisement

Ana Zargin Jami’an Ƴansanda Sun Buɗe Wuta A Kan Masu Zanga Zangar Lumana A Lagos 

Bidiyon da ke yawo ya nuna yadda tayar ke faɗowa daga ɓangaren baya na na’urar sauka da tashi (landing gear) a daidai lokacin da jirgin ke ɗagawa sama.

Advertisement

Sai dai, duk da faruwar lamarin, jirgin ya ci gaba da tafiyarsa cikin aminci zuwa Landan, inda ya sauka lafiya ba tare da wata matsala ba, kamar yadda bayanan shafin Flightradar24 suka nuna. Rahoton ya ƙara da cewa jirgin ya isa Landan mintuna 27 kafin lokacin da aka tsara.

Har yanzu dai ba a bayyana musabbabin da ya haddasa ɓallewar tayar ba.

Advertisement

A wata sanarwa, kamfanin British Airways ya ce tsaro shi ne ginshiƙin dukkan ayyukansa, kuma yana ba da cikakken haɗin kai ga hukumomin da ke gudanar da bincike kan lamarin.

Haka kuma, Filin Jirgin Sama na Harry Reid ya tabbatar da cewa an kwashe tayar daga filin jirgin, tare da jaddada cewa ba a samu rahoton jikkata ko lalata dukiyar filin jirgin sama ba.

Advertisement

 

SKY NEWS

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending