Connect with us

News

An Gurbata Harkar Tsaro Da Siyasa A Najeriya  — Lawal Daura

Published

on

102864198 dkabhzeucaarofm.jpg

Tsohon Shugaban Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), Alhaji Lawal Daura, ya ce cuɗanya harkar tsaro da siyasa na daga cikin manyan dalilan da ke sa Najeriya ke ci gaba da fuskantar matsalolin rashin tsaro.

Daura ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da gidan rediyon RFI, inda ya ce tsoma bakin siyasa da fifita son rai a harkokin tsaro na raunana ƙoƙarin hukumomi wajen yaƙi da matsalolin tsaro.

Advertisement

Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Nuna Alhini Kan Rasuwar Mutane 30 A Hatsarin Mota A Kano 

A cewarsa, maimakon a bar ƙwararrun jami’an tsaro su yi aikinsu bisa ƙa’ida da ƙwarewa, ana yawan sanya siyasa da alaka ta kashin kai a gaba, lamarin da ke bai wa masu aikata laifuka damar ci gaba da addabar jama’a.

Advertisement

Tsohon shugaban na DSS ya jaddada cewa magance matsalar tsaro na buƙatar tsari mai zaman kansa, gaskiya da kuma yanke hukunci bisa bayanan sirri na ƙwarai, ba tare da la’akari da wata fa’ida ta siyasa ba.

Kalaman Lawal Daura na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriya ke fuskantar ƙalubalen tsaro da suka haɗa da ta’addanci, garkuwa da mutane da kuma hare-hare a wasu sassan ƙasar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending