News
Kwankwasiyya Ta Karyata Zargin Amurka Kan Sanata Kwankwaso
Ƙungiyar Kwankwasiyya ta musanta rahotannin da ke nuna cewa kudiri da ke gaban Majalisar Dokokin Amurka, Nigeria Religious Freedom and Accountability Act 2026 (HR 7457), ya ambaci sunan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, a matsayin wanda ake zargi da take ‘yancin addini.
A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a ranar Alhamis, ta ce:
“Wannan zargi ba shi da tushe kuma ya saba da tarihin hidimar Sanata Kwankwaso.”
Sanarwar ta ƙara da cewa Kwankwaso ya shafe fiye da shekaru 30 yana hidima a manyan mukamai na ƙasa, ciki har da: Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Gwamna sau biyu na Kano, Ministan Tsaro, Sanata, da kuma ɗan takarar Shugaban Ƙasa.
Ƙungiyar ta jaddada cewa ba a taɓa gurfanar da shi a kotu kan zargin ta’addanci ko take haƙƙin ɗan Adam ba. Haka kuma, ta ce tsarin shari’ar Musulunci da aka kafa a wasu jihohin Arewa ba aikin Kwankwaso kaɗai ba ne, an yi shi ne bisa tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya, dokokin majalisa, da kulawar kotuna.
Kwankwasiyya ta roƙi Majalisar Dokokin Amurka da ta cire sunan Kwankwaso daga kudirin, tana mai cewa wasu na iya amfani da majalisar don biyan buƙatun siyasa ko na kashin kai.
