Connect with us

News

Ƴanbindiga sun hallaka mutane a wajen Tafsir

Published

on

Wasu da ake zargin Lakurawa be a ranar Laraba sun kai hari kan wasu da ke sallah a masallaci a garin Daɗin Kowa da ke ƙaramar hukumar Maiyama da ke jihar Kebbi inda suka kashe mutane 4 tare da raunata wasu da dama.

Mazauna garin sun ce maharan sun kewaye masallacin ne a yayin da ake Tafsirin Qur’ani da daddare inda suka buɗe wuta kan taron al’umma.

Advertisement

Gwamnatin Kano Ta Nemi Ƙara Ƙaimi Wajen Wayar da Jama’a Kan Nasarorin Gwamna A Manyan Makarantun Jihar 

Wani ma’aikacin lafiya da ya zanta da PREMIUM TIMES ya ce, waɗanda aka ji wa raunin an kai su asibiti domin samun kulawar gaggawa.

Advertisement

Biyo bayan harin, al’umma sun shiga alhini da fargaba. Sun ce hari ne na rashin imani da aka yi wa mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba da ke ibada a wata mai tsarki na Ramadana.

Har kawo lokacin da muke haɗa wannan rahoto, gwamnatin jihar ko jami’an tsaro ba su fitar da wani jawabi a hukunmance ba game da lamarin.

Advertisement

Bashir Usman, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, wanda muka yi ƙoƙarin tuntuɓa ba mu same shi ba saboda ba ya ɗaga wayarsa.

Lamarin dai ya faru ne bayan mako ɗaya da wani da ake zargin Lakurawa ne suka kai ƙaramar hukumar Arewa a jihar Kebbi wanda ya jaow mutuwar 34 da suka haɗa da matasa 23.

Advertisement

Irin waɗannan hare-hare a jihar na ƙaruwa inda ake kai wa masallata hari da gidajen ta hanyar ƙone su da sata da raba al’umma da matsuguninsu.

Sake ɓullar Lakurawa – ƙungiyar ‘yan ta’adda da ke da alaƙa da ‘yan ta’adda a ƙasashen yankin Sahel kamar Nijar da Mali – na ƙara ta’azzara matsalar tsaro a yankin Arewa maso yamma a Najeriya musamman a jihar Kebbi da Sakkwato.

Advertisement

Ga kuma wani hari da aka kai wa manyan dakarun sojin Najeriya a ranar 23 ga watan Fabarairu wanda PREMIUM TIMES ta rawaito yadda kwamadan runduna ta 8 kuma kwamandan runduna ta 2 ta rundunar haɗin guiwa ta ofureshan Fansan Yamma, Bemgha Koughna, wanda manjo-janar ne, ya tsallake rijiya da baya a jihar Kebbi.

Kwamandan ya tsira ne bayan da ‘yan ta’adda suka yi wa tawagarsa kwantan-ɓauna wanda ya jawo aka yi musayar wuta tare da kashe wasu daga cikin ‘yan ta’adda da ƙwace makamansu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending