Connect with us

News

Ministan Tsaron Ya Gayyaci Shugabannin Rundunonin Soji Kan Karuwar Hare-hare A Arewa

Published

on

Chris Musa (1)
Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya)

Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya gayyaci dukkan shugabannin rundunonin sojin Najeriya zuwa ofishinsa domin gudanar da wani muhimmin taro kan sababbin hare-haren da aka kai kan sansanonin soji daban-daban a yankin Arewa maso Gabas.

Waɗanda zasu halartar taron a hedikwatar Ma’aikatar Tsaro da ke Abuja sun haɗa da Babban Hafsan Tsaro, Janar Olufemi Oluyede, da Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu.

Advertisement

Ƴan Daba Sun Kashe Matashi Dan Kwamitin Tsaro A Kano

Sauran sun haɗa da Babban Hafsan Sojin Sama, Air Marshal Sunday Aneke, da Babban Hafsan Sojin Ruwa, Vice Admiral Idi Abass, tare da wakilai daga Hukumar Leken Asiri ta Ƙasa da sauransu.

Advertisement

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa a baya-bayan nan, ‘yan ta’adda sun kashe akalla kwamandoji uku na soji masu mukamin Laftanar-Kolonel a jihar Borno.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending