Connect with us

News

Jigawa: Gwamnati Ta Ƙara Alawus Ɗin Masu Unguwanni Zuwa N10,000

Published

on

Jigawa

Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da ƙara alawus ɗin da ake bai wa masu unguwanni a faɗin jihar daga naira dubu uku zuwa naira dubu goma a kowane wata.

An sanar da matakin ne bayan zaman majalisar zartarwar jihar da aka gudanar a Gidan Gwamnati da ke Dutse a ranar Talata, ƙarƙashin jagorancin gwamnan jihar, Umar Namadi.

Advertisement

Sifaniya Ta Janye Jakadiyarta Daga Isra’ila

Da yake yi wa manema labarai bayani kan sakamakon zaman, Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi na jihar, Dr. Nura Kazaure, ya ce ƙarin alawus ɗin na daga cikin matakan da gwamnatin jihar ke ɗauka domin ƙarfafa shugabannin gargajiya a matakin ƙasa wajen gudanar da ayyukansu.

Advertisement

A cewarsa, an ɗauki matakin ne duba da halin da tattalin arziki ke ciki, tare da la’akari da rawar da masu unguwanni ke takawa wajen hidimtawa al’umma da tallafa wa gwamnati a matakin ƙasa.

Masu unguwanni na daga cikin muhimman ginshiƙan shugabancin gargajiya, inda suke taka rawa wajen kula da harkokin al’umma, warware takaddama, da kuma taimakawa hukumomi wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya.

Advertisement

A fannin doka kuwa, kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 ya amince da rawar da sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma ke takawa a harkokin mulki.

Sashe na bakwai na kundin ya tanadi cewa gwamnatocin jihohi na iya shigar da masarautun gargajiya cikin harkokin kananan hukumomi a inda ya dace, yayin da sashe na takwas ya bai wa jihohi damar tsara dokokin da suka shafi kananan hukumomi da shugabancin gargajiya.

Advertisement

Sai dai kundin bai wajabta biyan albashi ga masu rike da mukaman gargajiya ba, lamarin da ya sa biyan alawus-alawus ga masu unguwanni ya kasance lamari da kowace jiha ke tsara shi bisa dokokinta.

A wasu jihohin Najeriya kuma, hakimai na karɓar alawus da ya kai tsakanin naira 26,000 zuwa sama da naira 90,000 a kowane wata, gwargwadon tsarin jihar da kuma tsawon lokacin da suka yi a kan mukami.

Advertisement

 

PUNCH

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending