News
Shugaba Tinubu Ya Mayar Da Hankali Kan Zaɓen 2027 Yanzu, Ya Manta Da Batun Tsaro Da Walwalar Jama’a —Ndume

Sanatan mai wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume, ya zargi gwamnatin tarayya da sakaci wajen magance matsalar tsaro, yana mai cewa hankalinta ya fi karkata kan siyasar zaɓen 2027 maimakon kare rayuka da walwalar jama’a.
Ndume ya bayyana hakan ne a ranar Talata, bayan jerin hare-haren bam da suka auku a Maiduguri, babban birnin jihar Borno, inda aka kai hare-hare a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri (UMTH) da kasuwar Monday Market.
Hatsarin Jirgin Sama Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane A Ghana
Rahotanni sun ce hare-haren sun yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 23, tare da jikkatar sama da 100, lamarin da ya sake tayar da hankulan jama’a a yankin Arewa maso Gabas. Jami’an tsaro sun alakanta harin da mayaƙan Boko Haram.
Haka kuma, an ruwaito wasu hare-hare a yankunan Ajari, Baga da Damboa, yayin da aka kai wani hari a Ngoshe da ke ƙaramar hukumar Gwoza, inda ake zargin haɗin gwiwar Boko Haram da ISWAP suka kashe jami’an tsaro da wasu shugabannin al’umma, tare da sace mata da yara.
‘Gwamnati na rasa amincewar jama’a’
Ndume ya ce gazawar gwamnati wajen ɗaukar matakin da ya dace na iya jefa ta cikin rashin amincewar jama’a.
“A maimakon mayar da hankali kan tsaron al’umma, sai muka rungumi siyasa, alhali mutanen da za su zaɓe mu na ci gaba da mutuwa,” in ji shi.
Sanatan ya ƙara da cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu na karkatar da hankali zuwa batun zaɓen 2027, wanda ya ce bai kamata ya zama abin da ya fi muhimmanci a wannan lokaci ba.
Ya kuma gargadi jam’iyyar APC cewa idan ba a inganta tsaro da walwalar jama’a ba, mutane na iya juya mata baya.
“Idan aka kasa samar da tsaro da jin daɗin jama’a, mutane za su fara kallon gwamnati a matsayin maƙiyiyarsu,” in ji Ndume.
Kira ga ƙarin matakan tsaro
Sanatan ya bukaci jami’an tsaro su ƙarfafa tattara bayanan sirri da kuma matakan dakile hare-hare, tare da gano waɗanda suka kai harin bam a Maiduguri domin hukunta su.
Ya ce akwai yiwuwar gano wanda ya kai harin, musamman ganin cewa an ɗauke shi a cikin babur mai ƙafa uku, wanda zai iya taimaka wa bincike.
Ndume ya bayyana matakan da gwamnati ke ɗauka a halin yanzu a matsayin marasa gamsarwa.
Har ila yau, ya bukaci mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, da ya kai ziyara jihar Borno domin jajanta wa al’umma da kuma duba halin da suke ciki, idan shugaban ƙasa ba zai samu damar hakan ba.
Ci gaba da barazanar Boko Haram
Tun daga shekarar 2009 ne rikicin Boko Haram ya fara a yankin Arewa maso Gabas, musamman a jihar Borno. Duk da nasarorin da jami’an tsaro suka samu a wasu lokuta, har yanzu hare-haren na ci gaba da jefa al’umma cikin fargaba.
Ana zargin sabbin hare-haren na da alaƙa da wani kwamandan ƙungiyar mai suna Ali Ngulde, wanda ake dangantawa da hare-hare a yankunan Gwoza da Pulka, ciki har da waɗanda suka yi sanadin mutuwar jami’an tsaro da fararen hula da dama.
