News
Jami’an NDLEA Sun Kama Kunshi 510 Na Tabar Wiwi A Kano
Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa NDLEA ta sanar da kama kunshi 510 tabar wiwi tare da cafke wani mutum a Jihar Kano, gabanin bukukuwan ƙaramar Sallah.
A wata sanarwa da kakakin rundunar reshen Kano, Sadiq Muhammad-Maigatari, ya fitar, ya ce an kama wanda ake zargin ne a ranar 10 ga watan Maris bayan wani samame da jami’an suka kai bisa samun bayanan sirri.
An Gudanar Da Sallah Idi A Sakkwato
Mutumin mai suna Sani Musa, mai shekaru 34, ɗan asalin ƙaramar hukumar Bebeji, an same shi da kunshi 510 na tabar wiwi da aka matse.
A cewar NDLEA, wanda ake zargin ya amsa cewa wani dillalin miyagun ƙwayoyi da ake kira “Alaramma” ne ya ba shi kayan domin ya adana a gidansa, tare da bashi izinin sayar da su.
Hukumar ta ƙara da cewa an shirya sayar da wiwin ne a lokacin bakin Sallah.
NDLEA ta ce bincike na ci gaba domin cafke “Alaramma” wanda har yanzu yake tsere.
