News
Kotu Ta Yanke Wa Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Hukuncin Zaman Gidan Gyaran Hali Na tsawon Shekaru 15 A Kano
Kotu a Kano yanke wa wani dillalin miyagun ƙwayoyin da ake kira Jonathan Nuhu, mai shekara 45 da ke ƙauyen Kanke a Jihar Filato, hukuncin zaman gidan gyaran halin ne na tsawon shekaru 15 sakamakon samunsa da laifin mallakar tabar wiwi.
Rahotanni na nuni da cewa wannan hukunci zai fara aiki ne tun daga ranar da aka yankeshi.
Kakakin Hukumar yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA), reshen jihar Kano, Sadiq Muhammad Maigatari ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.
Sadiq Ya kuma bayyana cewa Babbar Kotun Tarayya da ke Kano, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a MN Yunusa ne ya yanke hukuncin a ranar 17 ga Maris, 2026.
Ya kuma bayyana cewa, jami’an NDLEA sun kama Nuhu ne tun a ranar 20 ga watan Yulin shekarar 2023, a kusa da gadar Wudil da ke ƙaramar hukumar Wudil a Jihar Kano, biyo bayan cafke buhunan tabar wiwi guda 116 da aka samu a wurinsa.
Sanarwar ta ƙara da cewa, “An gaggauta gurfanar da shi gaban kotu, bayan shafe shekaru uku ana bincike da shari’a, kotun ta same shi da laifin da ake tuhumarsa da aikatawa tare da yanke masa hukuncin zaman gidan yarin.”
Maigatari ya ci gaba da cewa, akwai bayanan da ke nuna cewa a baya ma Babbar Kotun Tarayya da ke Jihar Jigawa ta taɓa yanke wa Nuhu hukuncin shekaru 15 a gidan yari ranar 22 ga watan Yunin shekarar 2021, kan makamancin wannan laifi.
A lokacin da aka kama shi da sabon laifin a Kano, yana waje ne a kan belin da aka ba shi yayin da yake jiran sakamakon ɗaukaka ƙara kan shari’arsa ta farko, lamarin da ya kai ga sake yanke masa wannan sabon hukuncin.
