Connect with us

News

Jaridar Inda Ranka Na Taya Daukacin Al’ummar Musulmi Murnar Zagayowar Sallah Karama Da Aka Fi Sa-ni Da Eid-el-Fitr

Published

on

IMG 20260320 095902 934

Jaridar Inda Ranka ta taya al’ummar Musulmi a Najeriya da ma duniya baki ɗaya murnar zagayowar bikin Ƙaramar Sallah, wato Eid-el-Fitr, bayan kammala azumin watan Ramadan na shekarar 1447 bayan hijirar Annabi Muhammad (SAW).

‎A cikin wata sanarwa da Shugaban Jaridar, Kabiru Basiru Fulatan, ya rattabawa hannu a ranar Jumma,a, jaridar ta nuna godiyarta ga Allah bisa bai wa al’umma damar kammala ibadar azumi cikin kwanciyar hankali.

Advertisement

Zaben 2027: Kungiyar Tinubu Uba Sani Sun Nuna Goyon Bayansu Ga Dan Buran a Kujerar Sanatan Kaduna Shiyya Ta Daya.

‎Sanarwar ta ƙara da cewa an yi addu’ar Allah Ya karɓi ibadun Musulmi, Ya gafarta kura-kuransu, tare da samar da zaman lafiya da ci gaba a ƙasar nan.

Advertisement

‎Jaridar ta kuma bayyana fatan Allah Ya maimaita wannan lokaci cikin koshin lafiya da yalwar arziki ga al’ummar Musulmi.

IMG 20260320 WA0009

‎Shugaban jaridar ya jaddada cewa Inda Ranka na da burin inganta addinin Musulunci ta hanyar shirye-shirye da tattaunawa da malamai, domin ƙara wayar da kan al’umma da kuma shiryar da su zuwa ga tafarkin alheri.

Advertisement

‎Haka kuma, sanarwar ta yi kira ga al’ummar Najeriya da su ci gaba da haɗa kai, tare da yin aiki tukuru domin samun yardar Allah, zaman lafiya da kuma bunƙasar ƙasa.

‎“Najeriya ƙasa ce da za a iya gina ta idan aka haɗa kai,” in ji sanarwar.

Advertisement

‎A ƙarshe, jaridar ta buƙaci Musulmi da su ci gaba da riƙe kyawawan ɗabi’u da ayyukan alheri da suka koya a watan Ramadan, tare da yaba wa ma’aikatanta bisa ƙoƙarinsu, inda ta yi musu fatan samun albarka da kariyar Allah.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending