News
Ƙungiyar KDF Ta Jinjinawa Gwamnatin Kano Bisa Tabbatar Da Tsaro A Lokacin Bukukuwan Sallah
Ƙungiyar Kano Development Forum (KDF) ta yaba wa Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf kan matakin da ta ɗauka na tabbatar da tsaro da zaman lafiya yayin bukukuwan bikin Ƙaramar Sallah, wato Eid-el-Fitr
A cikin wata sanarwa da Kodinetantan Kungiyar , Dakta Tanimu Adam Ibrahim, ya fitar, ƙungiyar ta bayyana matakin a matsayin wanda ya dace.
Sanarwar kara da cewa Gwamnan Kano ya nuna yadda gwamnati ke ƙoƙarin daidaita kiyaye al’adu da kuma kare lafiyar al’umma.
Ƙungiyar ta kuma yabawa Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, bisa yadda ya nuna haƙuri da bin doka wajen amincewa da matakan cikin natsuwa, tana mai cewa hakan abin koyi ne ga jama’a.
KDF ta yi kira ga al’ummar Kano State da su gudanar da bukukuwan Sallah cikin lumana, su ba jami’an tsaro haɗin kai, tare da kauce wa duk wani abu da ka iya haddasa tashin hankali.
Ƙungiyar ta kuma taya Musulmi murnar Sallah, tare da fatan zaman lafiya da ci gaba a ƙasar.
