News
HAWAN NASARAWA:Gwamnan Kano Ya Musanta Zargin Yin Watsi Da Sarki Sanusi II
Gwamnatin Jihar Kano ta musanta zarge-zargen da ke yawo a wasu kafafen yada labarai cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi watsi da Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, yayin hawan Nasarawa.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, ya bayyana zargin a matsayin “ƙarya mara tushe” da aka ƙirƙiro domin yaudarar al’umma da kuma tayar da hankali.
Hadimin Gaduje Ya Fice Daga APC Zuwa ADC
Sanarwar ta ce rashin halartar gwamnan a wajen hawan ya samo asali ne daga cunkoson jadawalin aikinsa, wanda ya tilasta masa fita daga jihar domin halartar wasu muhimman al’amura, ciki har da tarurrukan da suka shafi Sallah a matakin ƙasa.
Ta kuma ƙara da cewa gwamnan ya sanar da Sarkin Kano halin da ake ciki tun kafin tafiyarsa, inda ya umurci wasu manyan jami’an gwamnati, ciki har da kakakin Majalisar Dokokin Jihar, da su wakilce shi wajen tarbar sarkin.
Gwamnatin ta jaddada cewa babu wata matsala tsakanin ta da Masarautar Kano, tare da kira ga jama’a da su yi watsi da rahotannin da ta kira na ƙarya, su kuma rika dogaro da sahihan hanyoyin samun labarai.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
