Connect with us

News

Jami’an NDLEA Sun Kama Miyagun Kwayoyi Da Aka Ɓoye A Jaket Da Man Shafawa A Filin Jirgin Saman Legas

Published

on

1774238697763

Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta sanar da dakile wani yunƙurin safarar miyagun kwayoyi zuwa ƙasar Italiya, bayan gano su ɓoye cikin jaket na sanyi da kwalaben man shafawa a Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed da ke Legas.

A cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Femi Babafemi, ya fitar a ranar Lahadi, ya ce jami’an NDLEA sun gano haramtattun kwayoyin a wasu kayayyaki da ake shirin fitarwa ta jirgin sama, ciki har da waɗanda aka ɓoye a cikin kwali da kuma kayayyakin shafawa.

Advertisement

Ydda Mutane Suka Je Ɗiban Ganima Bayan Faɗuwar Tankar Man Fetur A Ibadan

Sanarwar ta ƙara da cewa an cafke wani mutum mai suna Friday Ehianuka, mai shekaru 37, a ranar Juma’a 20 ga watan Maris, 2026, yayin da yake ƙoƙarin tafiya zuwa birnin Rome na ƙasar Italiya ta jirgin Ethiopian Airlines.

Advertisement

Haka kuma, hukumar ta ce ta kama wasu karin mutane biyu da ake zargi da hannu a safarar, bayan gano wasu kayayyaki guda biyu da aka shirya aikawa ƙasar Italiya.

NDLEA ta jaddada cewa za ta ci gaba da tsaurara matakai domin hana safarar miyagun kwayoyi, tare da kira ga jama’a da su bai wa jami’an tsaro haɗin kai wajen yaƙi da wannan matsala.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending