News
Dakarun Soji Sun Ceto Wata Mata Tare Da Kama Waɗanda Su Ka Yi Garkuwa
Dakarun rundunar Operation Whirl Stroke (OPWS) sun ceto wata mata mai shekaru 28 mai suna Misis Member Ityavber a ƙauyen Tse-Ubena da ke gundumar Yooyo a ƙaramar hukumar Katsina-Ala ta jihar Benue.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mukaddashin jami’in yaɗa labarai na OPWS, Laftanar Ahmad Zubairu, ya fitar kuma aka rabawa manema labarai a ranar Alhamis.
Matar Da Ta Haifi ‘Ya ‘Ya Biyar A Asibitin Murtala Ta Rasu.
A cewar Laftanar Zubairu, an gudanar da aikin ceton ne tare da haɗin gwiwar rundunar tsaron jihar da ake kira Benue Civil Protection Guard.
Mai magana da yawun rundunar ta OPWS ya ƙara da cewa, an kuma kama wasu mutum biyu da ake zargi da kasancewa makiyaya masu ɗauke da makamai a yankunan Mbapa da Mbabuande da ke ƙaramar hukumar Gwer West ta jihar.
Laftanar Zubairu ya ce dakarun sun gudanar da aikin ne bisa ingantaccen bayanan sirri, inda suka yi bincike mai zurfi tare da gano wani wuri da ake zargin maboyar masu aikata laifi ce, wadda aka tarar an yashe ta.
