News
An Sanya Dokar Hana Fita Ta Sa’o’i 48 A Jos

Gwamnatin Jihar Filato ta sanar da ƙaddamar da dokar hana fita ta sa’o’i 48 a Jos ta Arewa. Matakin ya biyo bayan wani hari da ya auku a Gari Ya Waje ranar Lahadi, 29 ga Maris, 2026.
A cewar sanarwar, dokar za ta fara aiki daga ƙarfe 12 na dare na 29 ga Maris. Za ta ƙare ranar 1 ga Afrilu, 2026, domin bai wa jami’an tsaro damar daidaita al’amura.
Sheikh Pantami Ya Roƙi El-Rufai, Ribadu Da Uba Sani Su Sulhunta A Jana’izar Mahaifiyarsa
Gwamnatin jihar, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Caleb Mutfwang, ta yi Allah-wadai da harin. Ta ce za a kamo masu hannu cikinsa tare da gurfanar da su gaban shari’a.
Hukumomi sun buƙaci jama’a su kwantar da hankula su kuma bi umarnin tsaro. An roƙe su su ba da bayanai masu amfani don taimaka wa bincike.
Sanarwar da Kwamishinar Yaɗa Labarai, Joyce Ramnap, ta sanya wa hannu ta jaddada ƙudirin gwamnati na kare rayuka da dukiyoyi.
-
News3 days ago
Wasu ’Yanbindiga Sun Yi Garkuwa Kimanin Yara 12 A Neja
-
News21 hours ago
Majalisar Dattawa Ta Yi Watsi Da Shirin Farfaɗo Da Kamfanin Jirgin Saman Nigeria Air
-
News3 days ago
Jami’an NDLEA Sun Kama ‘Yan Nijeriya Biyu Mazauna Turai Da Suka Haɗiye Ƙunshin Hodar Iblis Guda 200 A Filin Jirgin Abuja
