News
Shugaban NUJ Ya Yaba Da Aikin Kano Correspondents’ Chapel, Ya Kira ‘Yan Jarida Su Kara Hadin Kai

Shugaban ƙasa na Alhassan Yahya, ya yaba wa shugabannin ƙungiyar Kano Correspondents’ Chapel, NUJ saboda kafa ginshikin da ke karfafa kauna, hadin kai, da ci gaba a tsakanin ‘yan jarida a jihar Kano.
Kwamared Yahya ya bayyana wannan ne a Cibiyar ‘Yan Jarida ta Kano a ranar Lahadi, a yayin taron walimar cin abinci da godiya ga Allah da ‘yan jaridar suka shirya bayan kammala Ibadar Azumin watan Ramadhana da kuma bukin Sallah.
Jami’an NDLEA Sun Kama Hodar Iblis Da Aka Ɓoye A Cikin Kan Kifi
A jawabin sa, Shugaban NUJ ya bukaci mambobin kungiyar su ci gaba da amfani da darussan da suka koya a watan Ramadhana, musamman dabbaka hadin kai, zaman lafiya, da hakuri yayin gudanar da ayyukansu na yau da kullum.
Hakanan, Kwamared Yahya ya samu wakilcin tsohon shugaban NUJ reshen Kano kuma mamba a Kwamitin Amintattu na NUJ, Abbas Ibrahim, wanda ya bayyana cewa a karkashin jagorancin Murtala Adewale, an samu gagarumin ci gaba a cikin shekara guda, musamman a ayyukan da suka shafi al’umma.
Kwamared Ibrahim ya kara jaddada muhimmancin nuna kauna da hadin kai a tsakanin ‘yan jarida wajen fuskantar kalubale na samar da abinci, kiwon lafiya, da tsaron al’umma.
-
News4 days agoWasu ’Yanbindiga Sun Yi Garkuwa Kimanin Yara 12 A Neja
-
News1 day ago
Majalisar Dattawa Ta Yi Watsi Da Shirin Farfaɗo Da Kamfanin Jirgin Saman Nigeria Air
-
News4 days agoJami’an NDLEA Sun Kama ‘Yan Nijeriya Biyu Mazauna Turai Da Suka Haɗiye Ƙunshin Hodar Iblis Guda 200 A Filin Jirgin Abuja
