Connect with us

News

Jama’a Sun Hallaka Barawon Waya A Kano

Published

on

Hukumomi a Najeriya sun tsaurara matakan tsaro da kuma sa ido sosai a birnin Kano,

Dubun wasu matasa biyu da ake zargi da satar waya ta cika, bayan da taron jama’a ya afka musu a kusa da makarantar Fatima Special Primary School, da ke unguwar Gyadi-Gyadi, a gaban ƙofar Asibitin Koyarwa na Aminu Kano.

Shaidu sun ce wata da farko matasan sun far wa wata budurwa da wuka, inda saboda tsoron kada su kai mata hari, ta mika musu wayar salim-alim.

Advertisement

Gwamnatin Filato Ta Sassauta Dokar Takaita Zirga-zirga Da Ta Sa A Jos

Bayan haka, sai suka kai wa wani mutum da ke wucewa hari suka kwace wayarsa. Wannan ne ya jawo hankalin masu wucewa, suka yi ƙarfin hali suka fuskance su.

Advertisement

Wani mai harkar POS a kusa da Court Road Roundabout ya ce matasan sun fito da wukake suna barazanar duk wanda ya kuskura ya matso su za su yi masa lahani, abin da ya fusata jama’a.

A cikin dan lokaci taron jama’a ya afka musu, aka yi musu dukan kawo wuka da duk abin da aka samu.

Advertisement

Ya ce: “Ba wannan ne karo na farko da masu satar waya suka addabi mutane a nan ba. Mutane sun gaji da irin wannan, shi ya sa lokacin da waɗannan matasan suka kwace wayar yarinya da ta wani mutum, jama’a suka afka musu.

“Mun ga yadda aka yi musu duka har suka suma, daga baya aka ce ɗaya daga cikinsu ya rasu a asibiti bayan an kai shi daga wurin.”

Advertisement

Wani shaidu ya ce yana dawowa daga Naibawa ne lokacin da ya ci karo da taron taron jama’a a kusa da Court Road Roundabout.

Ya ce: “Na ga matasan an yi musu jina-jina. Matasa ne ’yan kimanin shekaru 20 zuwa 25.”

Advertisement

 

 

Advertisement

AMINIYA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending