News
KANO: Jinkirin Diyya Ya Jefa Manoma A Albasu Cikin Mawuyacin Hali
A jihar Kano, manoma a ƙaramar hukumar Albasu sun bayyana damuwa kan jinkirin biyan diyya bayan aikin gina hanyar Hungu zuwa Dalawa da ya shafi gonakinsu.
Manoman sun ce aikin da aka fara a bara ya lalata gonaki da dama, lamarin da ya jefa su cikin matsin tattalin arziki, inda da yawa ke fama da wahalar ciyar da iyalansu.
Shugaba Tinubu Ya Amince Da Ware Tiriliyan 3.3 Domin Biyan Bashin Wutar lantarki A Najeriya
Ɗaya daga cikin manoman da abin ya shafa, Kawu Hassan, ya shaida cewa tun bayan da aka fara aikin, bai sake iya noma gonarsa ba.
Ya ce, “Ba a biya mu diyya ba duk da alkawarin da aka yi. Wannan ya jefa iyalina cikin wahala.”
Hassan ya kuma yi zargin cewa wasu jami’ai na kokarin hana su neman hakkokinsu, duk da cewa su manoma ne masu neman adalci.
A nata bangaren, wata bazawara, Hajiya Yelwa, ta ce jinkirin diyya na kara tsananta rayuwar marayunta.
Ta bayyana cewa, “Yanzu muna rayuwa ne da taimako, saboda gonata na cikin wadanda aka lalata amma ba a biya ni diyya ba.”
Wani dattijo, Mobi, shi ma ya nuna takaicinsa kan jinkirin, yana mai cewa sun dade suna jiran a biya su hakkokinsu ba tare da samun mafita ba.
Manoman sun kuma yi kira ga gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da ya shiga tsakani domin tabbatar da an biya su cikin gaggawa.
Sai dai shugaban ƙaramar hukumar Albasu, Garba Aliyu Hungu, ya musanta zargin tsoratarwa, yana mai cewa jinkirin ya faru ne sakamakon rashin sakin kudade daga gwamnatin jihar.
Ya ce da zarar an saki kudaden, za a biya duk manoman da abin ya shafa.
Rahotanni sun nuna cewa kimanin manoma 54 ne wannan matsala ta shafa, kuma har yanzu suna jiran a biya su diyya.
