News
Shugaba Tinubu Ya Amince Da Ware Tiriliyan 3.3 Domin Biyan Bashin Wutar lantarki A Najeriya
Shugaba Bola Tinubu ya amince da wani tsari na biyan tsohon bashin Naira tiriliyan 3.3 da nufin gyara matsalar wutar lantarki a Nijeriya da akajima ana fama da ita.
A wata sanarwa da Kakakin Shugaban ƙasa Bayo Onanuga ya fitar, an ce bashin ya samo asali ne tun daga watan Fabrairun 2015 zuwa Maris 2025, kuma an amince da wannan adadi ne bayan tantancewa domin tabbatar da adalci wajen biyan sa.
Kano: Gwamnati Za Ta Bayyana Ayyukanta Domin Ƙara Goyon Bayan Jama’a
Tuni aka fara aiwatar da biyan bashin, wanda kimanin kamfanonin DisCos guda 15 ne aka yi yarjejeniyar da su akan Naira tiriliyan 2.3.
HakaHaka kuma, Gwamnatin Tarayya kawo yanzu ta haɗa biliyan N501 domin fara aiki akan al’amarin, wanda daga ciki har an biya su biliyan N223 kuma ana cigaba da biyan.
Ana sa ran wannan ci-gaba zai taimaka wajen daidaita al’amura a fannin wutar lantarki a Nijeriya musamman wajen inganta raba wuta daga DisCos da tabbatar da biya akan lokaci ga masu samar da gas, wanda babban ginshiƙi ne ga samar da ɗorewar lantarki a sassan ƙasar.
-
News1 day ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News2 days ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
