News
Duk ‘Yan Takarar Gwamnan Kano Babu Wanda Ya Fini Cancanta —Ali Amin Little Dan Takarar Gwamna A jam’iyyar ADC
Dan takarar gwamnan Jihar Kano a karkashin jam’iyyar ADC, Ibrahim Ali Amin Little, ya ce shi ne ya fi kowa cancanta da kwarewa a cikin ‘yan takarar da ke shirin fafatawa a zaben shekarar 2027.
Ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da manema labarai, inda ya ce yana da cikakken shiri da hangen nesa da zai bai wa jihar Kano sabuwar alkibla ta fuskar ci gaba.
Gwamnan Kano Ya Ce Mataimakinsa Ya Yi Ƙula-Ƙula Domin Ganin Ya Hamɓarar Da Shi Daga Kan Mulki
A cewarsa, da dama daga cikin masu neman kujerar gwamna sun taba rike mukamai daban-daban a baya, amma bai ga sun yi abin da ya kamata ba a lokacin da suke kan karagar mulki.
Ya kara da cewa hakan ne ya sa yake ganin al’ummar Kano ba za su sake ba irin wadannan mutane dama ba, domin a cewarsa lokaci ya yi da za a zabi shugabanni masu gaskiya da rikon amana.
Ali Amin Little ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su yi amfani da damar zabe wajen zabo shugabanni bisa cancanta da nagarta, ba tare da la’akari da son rai ko alaka ba.
Ya ce idan aka ba shi dama, zai mayar da hankali kan inganta harkokin ilimi, samar da ayyukan yi ga matasa, da kuma karfafa tsaro a duk fadin jihar.
Sai dai har yanzu ba a ji martanin sauran ‘yan takarar gwamna kan wadannan kalamai nasa ba.
