Connect with us

News

Zan Hakura Da Tsayawa Takara Daga Zaben 2027 —Atiku

Published

on

Atiku

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar, ya ce ba zai sake neman takarar shugaban ƙasar daga 2027 ba.

Ya ce idan aka yi la’akari da shekarunsa da kuma damar da yake da ita ba lallai ya ci gaba da neman damar daga shekara mai zuwa ba.

Advertisement

Jihohi 33 Da Al’ummomi Sama Da 14,000 Na Fuskantar Barazanar Ambaliya A 2026 — Gwamnatin Tarayya 

Atiku ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise a ranar Laraba.

Advertisement

Da aka tambaye shi game da cikarsa shekaru 80 a shekarar 2027 da yadda hakan zai iya daƙile masa damarsa, Atiku ya ce: “Tabbas za a samu ƙarin masu nema, kuma ita ce dama ta ƙarshe da zan fito takarar”

Atiku ya yi takarar shugaban ƙasar a lokuta da dama.

Advertisement

Ya nemi tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 1993 a karkashin jam’iyyar SDP inda daga baya ya bar wa Moshood Abiola, da kuma Action Congress a shekarar 2007, inda marigayi Umaru Musa Yar’Adua ya lashe zaɓen.

Atiku ya kuma tsaya takara a shekarar 2011 karkashin jam’iyyar ACN, inda ya sha kaye a hannun tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Advertisement

Ya koma jam’iyyar PDP ya tsaya takarar shugaban kasa a zaben 2019, inda ya sha kaye a hannun tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A 2023, ya sake fitowa takarar a PDP amma ya sha kaye a hannun Shugaba Bola Tinubu na APC.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending