News
MTN Ya Sanar Da Dakatar Da Tsarin Bayar Da Rancen Kati Da Data
Kamfanin sadarwa na MTN Nijeriya ya sanar da dakatar da tsarin bayar da rancen kati da data, wato Xtratime, na ɗan lokaci bayan sabbin ƙa’idoji da Hukumar Kare Gasa da jama’a (FCCPC) ta ƙaddamar. Kamfanin ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya aika wa Kasuwar Hannayen Jari ta Nijeriya a ranar Alhamis, yana mai cewa matakin ya zama dole domin bin sabbin dokoki na shekarar 2025.
Xtratime, wanda masu amfani da layukan biya kafin amfani ke yawan amfani da shi, yana bai wa kwastomomi damar aron kati ko data su biya daga baya lokacin da suka sake saka kuɗi. A cikin sanarwar da Sakataren Kamfanin, Uto Ukpanah, ya sanya wa hannu, MTN ta tabbatar da dakatarwar tare da cewa matakin na wucin gadi ne.
Karo Da Tsuntsaye Ya Tilastawa Jiragen Sama Biyu Saukar Gaggawa A Najeriya
Kamfanin ya bayyana cewa sabis ɗin yanzu ya shiga ƙarƙashin sabbin ƙa’idojin FCCPC da suka shafi ba da rance ta hanyar dijital, waɗanda ke buƙatar sabon lasisi da kuma bin tsauraran Sharuɗɗa. An ce wannan na daga cikin tsarin “Digital, Electronic, Online or Non-Traditional Consumer Lending Regulations, 2025” da ya ƙara faɗaɗa kulawa ga irin waɗannan ayyuka.
Duk da dakatarwar, MTN ta tabbatar wa abokan hulɗarta cewa har yanzu ana iya siyan kati da data ta hanyoyi daban-daban ba tare da wata matsala ba. Haka kuma ta rage muhimmancin tasirin matakin a harkar kuɗin shiga, tana mai cewa ba sa tsammanin zai yi wani babban tasiri ga kuɗaɗen kamfanin.
Sabbin ƙa’idojin FCCPC na shekarar 2025 sun ƙara tsaurara sa ido kan kamfanonin da ke bayar da rance ta hanyar dijital a Nijeriya, inda ake buƙatar su yi rijista da samun amincewa kafin ci gaba da aiki. An kafa wa kamfanoni wa’adin daidaitawa da dokokin zuwa watan Afrilu 2026, inda duk wanda bai bi ƙa’ida ba zai iya fuskantar hukunci, lamarin da ke nuna sabon mataki a kula da kasuwar rance a dijital da ke ƙara bunƙasa a ƙasar.
