Connect with us

News

Gobara Ta Lakume Albasar Sama Da Naira Miliyan 56 A  Sakkwato

Published

on

IMG 20260419 234036 929

Wata gobara da ta tashi a ƙauyen Kojiyo, da ke ƙaramar hukumar Goronyo a Jihar Sakkwato, ta lalata buhunan albasa akalla 2,275, lamarin da ya jefa manoma cikin matsanancin hali.

Rahotanni sun ce gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe biyu na rana a ranar Juma’a, inda ta shafe kusan sa’o’i bakwai tana ci kafin a shawo kanta. Duk da cewa ba a samu asarar rai ba, amma gobarar ta ƙone rumbunan adana albasa na gargajiya kimanin 65.

Advertisement

JAMB Ta Fitar Da Sakamakon Jarrabawar UTME Da Aka Yi A Ranakun Juma’a Da Asabar

Shugaban ƙungiyar masu noman albasa, sarrafawa da kasuwancinta ta ƙasa, Aliyu Isah Maitasamu, ya bayyana cewa kowanne rumbu na ɗauke da matsakaicin buhuna 35, wanda ya kai jimillar buhuna 2,275 da suka lalace.

Advertisement

Ya ce darajar kowanne buhu a kasuwa na kusan Naira 25,000, wanda hakan ya kai jimillar asarar kusan Naira miliyan 56.8.

Maitasamu ya ƙara da cewa har yanzu ba a tantance musabbabin gobarar ba, yana mai cewa ana ci gaba da bincike.

Advertisement

Sai dai ya ce wannan asara ba za ta haifar da tashin farashin albasa a kasuwa ba, domin yawan da ya ƙone bai kai girman da zai iya kawo sauyi a farashi ba.

Wasu daga cikin manoman da abin ya shafa sun bayyana damuwarsu. Abdullahi S. Rima, wanda ya rasa buhuna sama da 200, ya ce gobarar ta lalata masa duk abin da ya tara.

Advertisement

“Duk abin da na adana ya ƙone. Babban rashi ne sosai,” in ji shi.

Shi ma wani manomi, Nura Arzika Magaji, ya ce yanzu iyalinsa sun shiga halin ƙunci bayan rasa buhuna 70.

Advertisement

Sarkin ƙauyen Kojiyo, Muhammadu Sani Sarkin Rima, ya ce gobarar ta shafi gidaje da dama, inda wasu iyalai suka rasa hanyar samun abinci.

Ya yi kira ga gwamnati da hukumomin agaji da su kai dauki cikin gaggawa domin tallafa wa waɗanda abin ya shafa.

Advertisement

A nasa ɓangaren, jami’in hulɗa da jama’a na hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar (SEMA), Abdullahi Ghani, ya ce har yanzu ba su samu rahoton lamarin a hukumance ba, amma za su ɗauki mataki da zarar an sanar da su.

 

Advertisement

 

DAILY TRUST 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending