News
Rashin Kula Da Masu Buƙata Ta Musamman Ne Ke Janyo Yawaitar Mabarata A Arewacin Najeriya —Ganduje
Tsohon gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa rashin kulawa da aka yi wa Masu Buƙata ta Musamman ne ke haddasa yawaitar mabarata a yankin Arewacin Najeriya.
Ganduje ya bayyana hakan ne a ranar Jumma’a, 24 ga watan Afrilu, yayin bikin cika shekaru 10 da kafuwar ƙungiyar Let’s Talk Humanity da ke Kano, wadda ke mayar da hankali kan inganta damar samun ilimi ga kurame da makafi.
Wasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Mutum Uku Har lahira A Filato
Taron ya samu halartar masu ruwa da tsaki a fannin ilimin nakasassu, jami’an gwamnati da kuma ɗaliban da suka amfana da makarantar musamman ta Tudun Maliki, domin murnar cika shekaru goma ana fafutukar samar da ilimi ga kowa.
Ya ƙara da cewa shirye-shiryen da aka gabatar a wurin taron sun nuna cewa akwai damar samun sauyi mai kyau, idan gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki suka rungumi irin waɗannan tsare-tsare.
