Connect with us

News

Jami’an EFCC Sun Kama Ɗan Asalin Kamaru Bisa Zargin Damfarar Sama Da Naira Biliyan 1.5

Published

on

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya EFCC ta kama wani ɗan asalin ƙasar Kamaru mai suna Bekono Eric bisa zarginsa da aikata damfarar kuɗi da yawansu ya kai naira biliyan 1.5 da ta shafi bankin First Generation Bank.

Hukumar a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce an kama Mr Eric mai shekaru 47 a yankin Ikorodu na jihar Lagos, kuma kai tsaye ana zarginsa da zama jagoran gungun masu safarar kuɗaɗe da halasta kuɗaɗen haramun a tsakanin Najeriya da Kamaru.

Advertisement

DIYYAR NAIRA BILIYAN ƊAYA: Ko Kwandala Ba Zan Ba Yahaya Bello —Natasha Akpoti-Uduaghan

Da yake jawabi mai magana da yawun hukumar ta EFCC Dele Oyewale ya ce binciken farko ya gano cewa Mr Eric na cikin mutanen da ke aikata laifin damfarar bankuna da abokan hulɗar su ta hanyar amfani da katinsu na cirar kuɗi wato ATM Card.

Advertisement

A cikin sanarwar da hukumar ta fitar, ta ce irin waɗannan mutanen na buɗe asusun banki a Najeriya, su sami katin cirar kuɗi na ATM daga nan kuma sai su tsallaka zuwa makwaftan ƙasashe don aikata damfarar ta can.

Mr Oyewale ya ce da zarar an kammala bincike za’a miƙa wanda ake zargi a gaban kotu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending