News
Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Tantance Test Book Din Da Ake Amfani Da Su a Makarantu
Gwamnatin tarayya za ta ƙaddamar da sabon tsarin tantance littattafan da akekoyarwa a makarantun firamare da ƙananan makarantun sakandare da manyan makarantun sakandare a Nijeriya”
Cikin wata sanarwa da daraktar yada labaru da hulɗa da jama’a, na ma’aikatar Folasade Boriowo, ta fitar a jiya Lahadi.
Dogon Jira A Asibitocin Gwamnati Na Ci gaba da Jefa Marasa Lafiya cikin Wahala A Najeriya
Ma’aikatar Ilimi ta ce an ƙirƙiri wannan tsari ne domin dakile yawaitar littattafan da ba su da inganci tare da tabbatar da cewa ana amfani ne kawai da littattafan da suka dace da manhajar karatu kuma masu inganci a cikin makarantu.
Sanarwar ta ƙara da cewa hukumar da bincike da bunkasa Ilimi ta kasa (NERDC) za ta ci gaba da riƙe ikon amincewa da littattafan kamar yadda doka ta tanadar.
Hakazalika bayan an amince da littattafai, za a ci gaba da tantance su ta hanyar sabon tsarin jera su a matakin ƙasa domin zaɓar waɗanda suka fi dacewa ga kowane darasi da matakin karatu.
A cewar gwamnati, hukumar bincike da bunkasa ilimita kasa za ta kafa kwamitoci na dindindin na fannoni daban-daban da suka ƙunshi ƙwararru, domin gudanar da cikakken bincike bisa ƙa’idojin ilimi da koyarwa.
Sanarwar ta sake bayyana cewa duk wani littafi da ba a tantance shi kuma ba a saka shi cikin jerin wannan sabon tsari ba, ba za a amince a yi amfani da shi a makarantu ba, ko da kuwa an taɓa amincewa da shi a baya.
Haka kuma, ma’aikatar ta bayyana cewa za a fara aiwatar da wannan sabon tsari ne daga watan Satumba na shekarar 2026, bayan kammala tattaunawa da masu ruwa da tsaki da kuma tsara yadda tantancewar za ta kasance.
Gwamnatin tarayya ta sake jaddada aniyarta na inganta harkar koyo da kuma tabbatar da samar da ingantattun kayan karatu ga ɗalibai.
