Connect with us

News

Jami’an ‘Yansanda Sun Cafke Wani Mai Safarar Makamai A Kano

Published

on

IMG 20260510 160435 336

Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta ce ta samu nasarar kama wani da ake zargi da dillancin makamai tare da ƙwace bindigogi ƙirar AK-47 guda uku a hannunsa.

Kakakin rundunar na jihar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.

Advertisement

Mbappe Ba Zai Buga Wa Madrid Wasan El Clasico Ba

Kiyawa ya ce jami’ansu sun yi nasarar cafke wanda ake zargin yayin wani samame da suka kai unguwar Dandinshe da ke Ƙaramar Hukumar Dala.

Advertisement

Sanarwar ta ce an kama wanda ake zargi mai suna Umar Danladi Usman, mai shekaru 35, mazaunin Kurna Layin Masallacin a cikin wata mota ƙirar Honda Accord.

Sanarwar ta ƙara da cewa yayin tambayoyi, wanda ake zargin ya amsa cewa ya taho da bindigogin ne daga Ƙaramar Hukumar Dutsin-Ma ta Jihar Katsina.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending