Connect with us

News

Kotu Ta Aike Da Tsohon Ministan Lantarki, Saleh Mamman Gidan Yari Na Shekaru 75 

Published

on

FB IMG 1778669778178

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, hukuncin daurin shekaru 75 a gidan yari bayan samunsa da laifukan almundahana da halasta kudaden haram da suka kai Naira biliyan 33.8.

Hukumar Yaki da Masu Yi Wa Tattalin Arziki Ta’annati ta Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) ce ta gurfanar da tsohon ministan kan tuhume-tuhume guda 12 da suka shafi karkatar da kudaden gwamnati da kuma halasta kudaden haram.

Advertisement

Kotu Ta Hana Wani Babban Jami’in Gwamnati Zuwa Aiki Hajji 

Mai Shari’a James Omotosho, wanda ya jagoranci shari’ar, ya bayyana cewa kotun ta samu Mamman da laifi a dukkan tuhume-tuhumen da ake tuhumarsa da su.

Advertisement

Kotun ta yanke masa hukuncin daurin shekaru bakwai-bakwai kan tuhume guda 10, sannan ta kara masa shekaru uku da shekaru biyu kan tuhume na hudu da na biyar.

Mai shari’ar ya ce za a aiwatar da hukuncin ne a jere ba tare da zabin biyan tara ba, sai dai a tuhume na hudu inda aka ba shi damar biyan tarar Naira miliyan 10.

Advertisement

 

Haka kuma, kotun ta bayar da umarnin kwace wasu kudaden kasashen waje da aka gano daga hannunsa tare da wasu manyan kadarori guda hudu da ke Abuja da ake zargin suna da alaka da kudaden da ake bincike a kansu.

Advertisement

Tun a watan Yulin 2024 ne EFCC ta gurfanar da Saleh Mamman kan zargin hada baki da wasu jami’an Ma’aikatar Wutar Lantarki da wasu kamfanoni masu zaman kansu wajen karkatar da kudaden ayyukan madatsun ruwan lantarki na Zungeru da Mambilla.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending